‘Ana daƙile mata a siyasar Najeriya’Mata sanye da kayan gargajiya a lokacin bukin Ranar Mata ta Duniya ta 2023 a Legas

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mata sanye da kayan gargajiya a lokacin bukin Ranar Mata ta Duniya ta 2023 a Legas

Jakadiyar Birtaniya a Najeriya Catriona Laing ta ce an ƙi bai wa mata a ƙasar damar da ta kamata wajen ganin sun bayar da gudummawa domin ci gaban ƙasar.

Catriona Laing ta bayyana haka ne lokacin wata tattaunawa ta musamman da BBC, inda ta kuma nuna damuwa kan raguwar yawan matan da aka zaɓa ko bai wa muƙaman siyasa a gwamnatin Najeriya.

Ta lura da cewa yawan matan da suka samu nasarar cin zaɓe zuwa majalisar tarayya a zaɓen da aka kammala, ya ragu matuka idan aka kwatanta da zaɓen 2019.

Ta ce hakan ya mayar da Najeriya baya a ɓangaren siyasa.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like