Kungiyar bayar da agaji ta Red Cross Society reshen Jamhuriyar Nijar ta aika da ma’aikatanta 60 a yankunan da wata cuta ta bulla, wacce ta yi sanadin mutuwar akalla mutum 23.
Hukumomin kula da lafiya na kasar sun ce cutar, wadda ta ɓulla a yankin Tahoa, ana daukarta ne daga jikin dabbobi.
Sun kara da cewa mutum kimanin 60 ne suka kamu da ita tun daga tsakiyar watan Agusta.
Wasu jami’an ma’aikatar lafiya ta kasar sun shaida wa BBC cewa ana iya daukar cutar ta hanyar shan nonon dabbar da ke dauke da ita ko kuma idan sauro ya ciji mutum.
Haka kuma cutar tana sanya makanta da zubar da jini kafin mutum ya mutu.
Wasu rahotanni sun ce shanu da tumaki da kuma rakumai da dama ne suka mutu sanadin kamuwa da cutar.