
Asalin hoton, OTHERS
Gwamnatin Nijar ba ta ce komai ba kan ceto mutanen da Saudiyya za ta kashe
A jamhuriyar Nijar masu fafutukar kare hakkin dan’Adam sun bukaci gwamnatin kasar ta saka baki don dakatar da zartar da hukuncin kisa da kasar Saudiyya ke shirin yi kan wasu ‘yan Nijar hudu da ta kama da zargin fataucin miyagun kwayoyi.
Masu fafutukar na kokawa ne da yadda gwamnatin ta Nijar ta yi gum da bakinta suka ce akwai bukatar gwamnatin ta saka baki wajen ceto rayuwar mutanen.
Rahotanni sun bayyana cewa hukumomin Saudiyya sun damke maza biyu da mata biyu ne ‘yan Nijar a filin jirgin sama na Jeddah da ke kasar ta Saudiyya.
Ana zargin mutanen ne da fataucin miyagun kwayoyi da Saudiyyar ta haramta.
Al’umma a Nijar na tattauna batun a kafafen sada zumnta amma kawo yanzu gwamnatin kasar ba ta ce uffan kan batun ba.
Dambaji Son Allah wani mai fafutukar kare hakkin bil’Adama ne a Nijar, ya ce akwai bukatar gwamnatin Nijar ta duba lamarin.
” Abu ne da Allah Ya kawo, idan hakan ya faru, ya kamata gwamnati ta fito ta yi wa mutane bayani dalla-dalla yanda lamarin ya faru da kuma yadda za ta kai dauki.”
Shi ma shugaban kungiyar kula da rayuwa a Nijar Hamidou Sidi Foudi ya ce “abun tashin hankali ne.”
“Duk dan’Adam din da ya ji labarin cewa cikin kwanaki kadan za a fitarwa dan uwansa rai dole hankalinsa ya tashi, a matsayinmu na masu kare hakkin bil’Adama ba za mu taba goyon baya a fidda wa dan’Adam rai ba”.
Foudi ya yi kira ga gwamnatin Nijar ta sanya baki don samun sulhu.
” Muna kira ga gwamnatin Nijar ta yi kokari ta aika tawaga don a samu sulhu bisa wannan matsalar.