Ana kashe-kashe a Sudan duk da sabunta batun tsagaita wuta | Labarai | DWKasashen Amirka da Saudiyya ne dai suka sanar da sabuwar yarjejeniyar, kasashen kuma da su ne suka shiga tsakani.

To sai dai kuma shaidu sun ce har yanzu ana ci gaba da kai wa juna hare-hare a Sudan din.

Tun a ranar Talatar da ta gabata ne bangarorin na Sudan suka sanya hannu kan wata yarjejeniyar da suka gaza mutuntawa.

Dukkanin su dai na zargin juna kan saba yarjejeniyar.

Fada ne dai da ke faruwa tsakanin shugaba mai rike da gwamnati Janar Abdel Fattah al-Burhan da mataimakinsa Mohammed Hamdan Daglo kusan makonni biyu yanzu.

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like