Ana Shirin Auran Zahra Buhari


 

Rahotanni masu karfi na nuna cewa ana shirye shiryen auran ‘yar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Zahra Buhari a watan Disambar shakarar nan a babban birnin tarayya Abuja.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa an sa ranar bikin ne a ranar Juma’a, 18 ga watan Nuwamba.

Zahra za ta auri Ahmad Indimi, da ga biloniyan dan kasuwan nan Mohammed Indimi kuma daraktan kasuwanci na kamfanin Oriental Energy Resource.

Bikin wanda za’a yi a ranar 2 ga watan Disamba zai kasance dan karami kuma mara hayaniya, tare da ‘yan uwa da abokan arziki na jikin iyalan amarya da ango, kamar yadda rahotan ya nuna.

 

You may also like