Ana shirin kashe El-Zakzaky da yi wa mabiyan mu kisan Kiyashi – Kungiyar ‘Yan uwa Musulmai


Kungiyar ‘yan uwa Musulmai (Shi’a) ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da Kakkausar murya da kada ta kuskura ta aiwatar da wani shirin ta da take yi a boye na neman kai wa mabiyan Kungiyar hari da ke fadin kasar nan.

Kakakin Kungiyar Ibrahim Musa ya ce akwai wata shiri da gwamnati take yi yanzu haka na kashe shugaban su Ibrahim El-Zakzaky da mabiyansu.

“ An tura jami’an tsaro garuruwan kasar nan domin shirin kai mana hari. Sannan ana shirin kashe shugaban mu Ibrahim El-Zakzaky.

Ibrahim Musa ya ce suna kira ga kungiyoyin kare hakkin dan Adam da su sa Ido akan wannan shiri sannan su kawo musu dauki.

“ Kashe shugaban mu Ibrahim El-Zakzaky ba zai yi wa Najeriya da mutanen ta kyau ba saboda haka dole ne gwamnati tayi nazari akan haka.”

Gwamnati na tsare da Ibrahim El-Zakzaky da matarsa tun a watan Disembar 2015.

You may also like