Ana shirin mayar da tubabbun mayaƙan Boko Haram 613 cikin al’umma



..

Asalin hoton, Nigeria Army

Hukumomi a Najeriya sun kammala shirin miƙa wasu  mayaƙan Boko Haram fiye da 600 da suka tuba ga gwamnatocin jihohinsu domin shigar da su cikin sauran al`umma.

Hedikwatar tsaron Najeriyar ta bayyana cewa an ɗauki wannan matakin ne  bayan an shigar da su cikin wani shirin gyara hali.

 Hafsan hafsoshin Najeriya, Janar Lucky Irabor ya bayyana cewa an kammala shirin miƙa mayakan Boko Haram ɗin da suka tuba su 613, bayan an gyara musu hali.

Ya yi bayanin ne a wajen wani taron masu hannu ko ruwa da tsaki a ƙarƙashin tsarin nan na ba da damar miƙa wuya ko tuba ga mayaƙan Boko Haram, wato Operation Safe Corridor.



Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like