
Asalin hoton, Getty Images
Duk da yake jima’i kafin aure babban abin kunya ne a Indiya, bincike ya nuna ana samun ƙaruwar matasa da ke yin hakan
Shekaru 10 da suka wuce, gwamnatin Indiya ta gabatar da wata doka mai tsauri don magance matsalar cin zarafin ƙananan yara ta hanyar lalata.
Yayin da dokar ta ƙunshi bai wa yaran kariya, da ayyana masu lalatar da aikata mugun laifi kan yara ‘yan ƙasa da shekara 18, yawancin matasa maza da ke tashen samartaka sun tsunduma wata harkar ta daban da ta saɓa wa dokar.
Kiraye-kirayen ɓullo da tsattsaurar doka na ƙaruwa kan samari da ‘yan mata, da nema ƙarara a haramta musu yin jima’i kafin aure.
Shekarun baya, lokacin da nake aiki game da wani rahoto kan tura wata ‘yar sanda kurtu, zuwa wani yanki da ake yawan aikata laifuka a wata gundumar birnin Delhi, sun je aikin ne domin bai wa mata karin kariya.
An kai ni wurin wata matashiya ‘yar shekara 16, wadda akai zargin an yi mata fyade.
”An yi wa wannan yarinyar fyade,” in ji ‘yar sandar lokacin da take nuna min yarinyar.
Amma lokacin da na tambayi yarinyar ko za ta ba ni labarin halin da ta samu kanta ciki, sai ta yi tsalle ta dire cewa sam ba a yi mata fyade ba.
”Cikin harshen Hindu ta kada baki ta ce: Main apni marzi se gayee thi, ma’ana bisa raɗin kaina na bi mutumin.”
A lokacin da mahaifiyar yrinyar ta fara yi mata faɗa, ‘yar sandar ta yi gaggawar janye ni daga gidan.
Iyayen yarinyar sun shigar da ƙarar wani ɗan makwaftansu, an kuma kama shi ana tuhumar sa da laifin fyade.
Ta amince alamu sun nuna suna soyayya da yaron, amma babu yadda ‘yan sanda za su iya, sai dai fa shigar da ƙara.
Shari’o’in da na gani a zahiri a shekarun baya, na cikin dubban da ake samun ‘yan matan Indiya da ake zargin an yi musu fyaɗe, soyayya ce suke yi kawai da ta kai su ga aukawa jima’i, sai a yi kwaskwarima a ce an aikata fyaɗe.
Ana buƙatar yin wata doka da ta yi kama da Pocso, saboda ƙaruwar cin zarafi ta hanyar lalata, kamar yadda ƙididdiga ta nuna a 2007, yayin da gwamnati ta ce an samu ƙaruwar hakan da kashi 53 cikin 100.
An kuma samu ƙaruwar matasa ‘yan shekara 16 zuwa 18 da soyayya ke jefa su wannan mummunan hali, hakan ya sa miliyoyin matasan da ke tashen balaga na samun kansu a gidan yari kan laifin yin lalata da matan.
Asalin hoton, Getty Images
Kotunan Indiya sun ce soyaya tsakanin yara ta sha bamban da ta balagaggu, waɗanda wani abu ne ya ja hankalinsu suka fara soyayyar
Indiya na da matasa sama da miliyan 253, ƙasa ce da ta yi fice da nau’o’i daban-daban na matasa a duniya, duk da yake jima’i kafin aure babban abin kunya ne, bincike ya nuna yawancin matasan na kan ganiyarsu.
Sama da kashi 39 na matan, sun shaida wa binciken da hukumar lafiyar iyali ta kasar ta jagoranta, kuma mafi inganci da gwamnati ta taɓa yi.
Kashi 10 na ma’auratan da ke tsakanin shekara 25 zuwa 49 sun ba da bahasin cewa sun taɓa yin jima’i kafin aure, wasu a ciki sun yi hakan suna ‘yan shekara 15.
A yanzu kiraye-kirayen ɗaukar matakin na ƙaruwa, a kuma rage shekarun zuwa 16 maimakon 18, kamar yadda sauran kasashen duniya ke yi, ciki har da ƙasashen yankin Asiya.
Masu rajin kare haƙƙin yara sun ce iyaye na amfani da dokar gwamnati, domin hana ‘yan matan yin soyayya, musamman wadanda suke da bambancin addini.
A karon farko an samu ƙididdiga kan matsalar
Wani bincike da asusun kula da lafiya na Enfold Proactive Health Trust ya fitar ya nuna wata ƙungiyar kare haƙƙin yara da ta yi binciken ta yi nazari a kan ƙararraki 7,064 da aka shigar kotun Pocso.
Ta kuma yanke hukuncin wasu a shekarar 2016 zuwa 2020 a jihohi uku na Indiya da suka haɗa da yammacin Bengal, da Assam da Maharashtra.
Kusan rabin ƙararrakin a kan mata ‘yan shekara 16 zuwa 18 ne aka shigar bisa zargin an yi musu fyaɗe.
Wani rahoto da aka fitar a farkon watan nan, ya gano ƙorafe-ƙorafe har 1,715 da kusan kashi ɗaya zuwa uku suna da alaƙa ta soyayya.
Idan kuma adadin ba a kasar Indiya ne kadai ba, tabbas za su iya kasancewa dubun-dubata a duk shekara.
”Ayyana yin jima’i tsakanin matasa a matsayin babban laifi, da wasu ke gani ba komai ba, ya nuna lamarin mai girma ne yanzu,” in ji shugabar masu bincike a Enfold Swagata Raha a hirarta da BBC.
Rahoton ya ce yawancin ƙararrakin, iyayen masoyan, ko dangi ne ke kai ƙorafe-ƙorafen, musamman idan masoyan sun tsere daga gida, ko mace ta yi ciki, nan da nan ‘yan sanda ke tusa ƙeyarsu kotu kan zargin aikata fyade, ko cin zarafi ta hanyar lalata ko ma sacewa domin neman kuɗin fansa.
”Wannan na sanya mutanen shiga tsaka mai wuya, yayin da kuma shari’a ta yi musu dabaibayi,” in ji Ms Raha.
Ta kuma ce irin wannan yanayin na janyo mace da namijin duk su fuskanci mummunan hukunci, yawanci sun tsere daga gida domin neman mafaka, domin kaunce wa zaman gidan kaso.
”Matan na jin kunya, da muzantawa, da tarin da-na-sani, ga wulakancin da za su fuskanta da tsangwama da wariya, suna gudun yadda za a zo ana kallon su, sun zama abin kwatance.
Don haka suke guduwa su nemi mafaka a sansanonin wucin gadi ko otal da sauransu.
Wadanda ake zargin na fuskantar bincike mai tsauri, za kuma su iya fukantar daurin shekara 10 zuwa 20 a gidan kaso idan har an same su da laifin,” in ji ta.
Asalin hoton, Getty Images
Indiya ta kasance ja gaba a duniya mai yawan matasa da suka kai sama da miliyan 253
“Ana samun mutane ƙalilan da ba a samun su da wani laifi, amma waɗanda ake samu da laifin sun kai kashi 93 da ya kasance masoya ne, kuma akan yi watsi da wasu ƙararrakin saboda rashin shaidu.
Dalilin da ya sa ake samun ƙarancin zartar da hukunci, shi ne matan na saurin cewa soyayya suke yi da mazan babu tilas ko takurawa a ciki, waɗanda ke amincewa da laifin kuwa takurawar ‘yan uwa ko iyaye ne ke janyo haka.
A shekarar 2019, lokacin da aka dakatar da zartar wa wata matashiya hukunci, alkalin babbar kotun mai shari’a V Parthiban, ya ce soyayya tsakanin kananan yara, ko karamar yarinya da babba ko matashi ba bakon lamari ba ne.
To amma ayyukan da ke biyo baya su ne abin damuwa. Don haka ya yi kiran a sake sabon lale.
A baya-bayan nan, Alkalin alkalan Indiya, Dhananjay Chandrachud ya yi karin bayani kan batun tare da kiran ‘yan majalisa su sake tunani da kuma rage shekarun balaga na 18 zuwa kasa da haka domin kaucewa cin zarafin kananan yaran.
Asusun kananan yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, Unicef ya damu matuka kan wannan matakin kan batun jima’in matasa gabannin aure.
Shugabar shirin bai wa ƙananan yaran kariya, Soledad Herrero, ta shaida wa BBC cewa ”Yara suna da damar bin hakkinsu, da ba su kariya, da damawa da su a fannin jin bahasinsu kan batutuwan da suka shafi hakkinsu”.
”Akwai bukatar kawo daidaito tsakanin ba da kariya da zartar da hukunci, a bambance tsakanin mai laifi da wanda ka yi wa laifin da dalilin aikata shi da kuma hanyar warwarewa.
Dole kwamitin Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin yara su san rawar da za su taka kan batun da ya shafi cin zarafi.”
Ms Raha ta kara da cewa fannin shari’a ya yi tsayin daka wajen tantance laifukan da aka aikata , da samun hadin kan fannin shari’a da wadanda abin ya shafa da ‘yan uwansu.
‘Yan majalisa na bukatar gabatar da wata doka, ”Muna kira ga ‘yan majalisa su sake nazari kan hukunta wadanda aka samu da yin jima’i gabannin aure, ya kamata mu gane ba sabon bu ba ne soyayya da jima’i tsakanin masoya.”