
Asalin hoton, Goal.com
Masoya ƙwallon ƙafa musamman masu goyon bayan Jr Neymar suna tofa albarkacin bakinsu a kafofin sada zumunta bayan ya yi asarar yuro miliyan ɗaya cikin minti guda.
Wani bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, ya nuna ɗan ƙwallon na yin cacar da ake kira (Poker) a turance cikin farin ciki da farko, kafin daga bisani ya fashe da kuka lokacin da tafka rashin nasara a wasan.
Sai dai wasu na ganin kukan da ɗan wasan gaban Brazil ɗin ya yi, kukan ƙarya ne, wanda wasu ke cewa bai kai zuci ba.
Yuro miliyan ɗaya ya yi a sarar a cacar daidai da kimanin naira miliyan 850 a canjin Najeriya.
Ɗan wasan PSG ɗin na cikin manyan ‘yan ƙwallon ƙafa a Turai da suka fi karɓar albashi mai yawa.
Ga dai abin da wasu masoya ƙwallo ƙafa ke cewa game da lamarin:
Shafin Loro ya ce Neymar ya yi asarar yuro miliyan ɗaya cikin awa guda, ɗan wasan gaban da ke fama da jinya a idon sawu, ya fara kaɗa cacar intanet. Kuma bayan an cinye shi, ya fashe da kuka, amma daga baya ya tuntisre da dariya… Ya tuna cewa kuɗin da ya yi asara ba wuce abin da ake biyan sa a cikin sati ɗaya ba.
Asarar yuro miliyan ɗaya cikin awa ɗaya tashin hankali ne a wajen kowa. Amma ga ɗan ƙwallo kamar Neymar, wannan ba komai ba ne. Duk da haka, ɗan wasan ya fashe da kukan ƙarya lokacin da yake cacar intanet ta kai tsaye a shafin Twitch, kamar yadda Gamohol ya bayyana.
Idan na yi asarar yuro miliyan ɗaya kamar yadda Neymar ya yi a cacar da ya buga a intanet zan shiga mugun tashin hankali, in ji Fiodor wani mai shafin Twitter.
Arsene Lapin cewa ya yi wannan wanne irin abin kunya ne “mutumin kawai ya sarayar da irin waɗannan kuɗaɗe” yayin da mutanen kirki ke ta fama da rayuwa da mafi ƙarancin albashi!
Kamata ya yi a matsa masa ya ƙara biyan haraji mai yawa.
A ranar 19 ga watan Fabrairu ne ɗan wasan ya ji rauni a idon sawunsa lokacin da yake buga wasan PSG da Lille.
Kwana guda bayan nan, ƙungiyar ta sanar da cewa Neymar zai yi jinya ta sama da wata huɗu kafin ya dawo atisaye.