Jami’an tsaro na farin kaya( DSS) sun bayyana cewa sun bankado wata makarkashiya da Gwamnan Rivers, Wike Nyeson da wani mai Taimaka Wa Shugaban Majalisar Dattawa na musamman mai suna Ikenga Ugochinyere da shirya na ingiza rikici a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Hukumar DSS ta kuma nuna cewa mutanen biyu sun shirya daukar hayar ‘yan daba don cimma wannan manufa inda suka tsara gudanar da zanga zanga a manyan hukumomin duniya da nufin nuna wa duniya cewa jami’an tsaro sun mamaye jihar Rivers.
Tuni dai, Shugaban. Majalisar Dattawa, Bukola Saraki ya nemi jami’an DSS kan sun gaggauta binciken mai taimaka masa na musamman inda ya jaddada cewa ba zai lamunci karya doka da oda ba.