
Asalin hoton, AFP
An kama ɗaruruwan mabiya cocin Orthodox a Habasha a ‘yan kwanakin nan bayan taƙaddamar da suke ta yi da hukumomi, kamar yadda lauyoyi da ke wakiltar cocin suka faɗa wa BBC.
Shugaban lauyoyi da ke wakiltar cocin na Orthodox, Ayalew Bitanie, ya ce zuwa yanzu an tsare mutane kusan 200.
Ya ce yawancin waɗanda aka tsaren, an ajiye su ne a Addis Ababa, babban birnin ƙasar, da wasu larduna da ke kusa da birnin, sai dai, an tafi da wasu zuwa wani sansanin soji da ke da nisan kilomita 200 da gabashin Addis Ababa.
Sai dai, BBC ba ta tabbatar da gaskiyar wannan iƙirarin ba.
Cikin waɗanda aka kama sun haɗa da jagororin matasa da wani sanannen mai wa’azi, in ji Ayalew.
An gabatar da wasu a gaban kotu a Addis Ababa, inda ‘yan sanda suka ce suna binciken waɗanda aka tsaren ko za a sam esu da laifuka da ke da alaƙa da ta’addanci da kuma yunkurin take dokar kundin tsarin mulki.
An fara zaman ɗar-ɗar ne bayan da wata kungiyar masu wa’azi da ta ware a yankin Oromia, ta naɗa malaman coci, inda jagororin cocin suka zargi hukumomi da mara wa kungiyar baya.
An shiga ruɗani bayan da cocin ta ɗage wani tattaki da ta shirya yi – a daidai lokacin da ƙasar ke shirin karɓar bakuncin taron kungiyar Haɗin Kan Afirka AU da aka saba yi duk shekara.
An takaita amfani da shafukan sada zumunta a ƙasar da suka haɗa da Facebok da Telegram da kuma YouTube.