Ana Tuhumar Wasu Mutane Biyu Da Laifin Fyade Da Kuma Yinkurin  Zubar Da Ciki 


Wani mutum dan shekara 30, Francis Okezie wanda ake zargi da laifin yiwa wata yarinya yar shekara 14 ciki sakamakon fyade da yayi mata ya gurfana a gaban kotun Majistire dake Ikeja a jihar Lagos a ranar Laraba.

 Ana tuhumarsa tare da Esther Udoh mai shekaru 32, wacce ake zarginta da bawa yarinyar maganin  zubar da ciki. 

Misata Okezie na zaune ne a yankin da ake kira Baruwa, Ipaja yayin da Udoh take zaune a Egbeda dake wajen birnin Lagos.

Mai gabatar da kara Raphael Donny ya shaidawa kotun cewa mutumin da ake zargi ya aikata laifin tsakanin watannin Janairu zuwa Yuni a  dakinsa dake gida daya da yarinyar. 

 “Mutum na farko da ake zargi yayiwa yarinyar fyade inda ta samu ciki inda ya dauki yarinyar zuwa wurin wacce ake zargi ta biyu  domin ta zubarwa da yarinyar cikin. 

“Wacce ake zargi ta biyu ta bawa yarinyar maganin ta sha domin  cikin ya zube.

” Bayan tasha maganin ne yarinyar ta fara zubar da jini,ba daban makota sun gani ba suka garzaya da ita asibiti da tuni yanzu yarinyar ta mutu. 

 Ankai rahoton faruwar lamarin wurin yan sanda inda aka kama mutanen biyu. 

Laifukan sun saba da sashi na 251 da kuma 259 na kundin dokar manyan laifuka ta jihar Lagos.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN, ya rawaito cewa daurin shekaru bakwai za ayi wa wanda yayi yinkurin zubar da ciki, yayin da za a yiwa wanda ya aikata fyade hukuncin daurin rai da rai.

Amma mutanen da ake zargi sun musalta zargin da ake musu.

Alkalin kotun majistire  Folakemi Davies Abegunde ya bada belin mai laifi ta biyu kan kudi naira 500,000 da kuma mutane biyu daza su tsaya mata. Yayin da aka tasa keyar mai laifi na farko zuwa gidan yari.

An dai dage shariar zuwa ranar 18 ga watan Satumba. 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like