Sanannen dan siyasar nan a Jamhuriya ta biyu a Najeriya, Dakta Junaidu Muhammad, ya bayyana cewa, Shugaba Muhammadu Buhari, na yi wa ‘yan Najeriya romon-baka kawai a yakin da ake yi da kungiyar mayakan Boko Haram.
A tattaunawarsa da manema labarai, Dakta Janaidu Muhammad, ya bayyana cewa, shugaban kasa da manya-manyan hafsoshin rundunar sojin Najeriya sun sha yin karya kan hakikanin halin da ake ciki a yaki da kungiyar ta BH, wannan ne ma ya sa bai yi mamakin sace ‘yan Matan makarantar sakandare ta Garin Dapchi da ke Jihar Yobe ba, a cewar Dakta Janaidu Muhammad.
.
“Wannan satar ‘yan Matan da aka yi na Garin Dapchi ta tabbatar cewa, babu tsaro a Najeriya, ya kuma nuna cewa abubuwan da ke fitowa daga fadar Shugaban kasa romon-baka ne kawai ba gaskiya ba,” kamar dai yadda Junaidu Muhammad ya bayyana.
Dakta Junaidu Muhammad ya kuma kara da cewa, a cikin nade-naden da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi cikin rundunar sojin Najeriya, ya yi su ne bisa son zuciyarsa bai duba cancanta ba.
Inda ya ce, mafita ga halin da tsaron Najeriya ke ciki ita ce, Shugaba Muhammadu Buhari ya sallami dukkanin manyan hafsoshin sojin Najeriya daga mukamansu, yana mai cewa matukar ba a yi hakan ba za ta taba sauya zani ba.