Ana yin zaman makoki a Mali


 

Gwamnatin Mali ta ayyana kwanaki uku na zaman mako tare da kara tsawaita dokar ta baci a kasar da kwanaki goma wacce ta kawo karshe tun a cikin watan Afrilun da ya gabata.

An soma yin zaman makokin ne na kwanki uku tun daga yau bayan wani harin da wasu ‘yan bindigar suka kai a kan wani barakin soji na Nampala,da ke a garin Segou wanda ke da nisa kilomita sama da 510 daga Bamako babban birnin kasar domin nuna alhini ga wadanda suka mutu har soji 17.

Barakin sojin na Segou shi ne na biyu mafi girma a Malin kuma shaidun sun ce ‘yan bindigar sai da suka karbi iko da rundunar na tsawo awowi da dama kafin daga bisani a ci karfinsu a harin da suka kai ranar Talata.Kana kuma wata sanarwa gwamnatin ta ce an tsawaita dokar ta baci da aka saka a duk fadin kasar tun a ciki watan Afrilu da gwanaki goma.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like