Ana Zargin DPO Na ‘Yan Sanda Da Yiwa Matasa Kisan Mummuke A Jihar Adamawa



Ana zargin DPO na ‘yan sanda ASP M. H Dass na Kiri a karamar hukumar Shelleng dake jihar Adamawa da yi wa wasu matasa makiyaya hudu kisan mummuke.
Wannan na kunshe a wata takardar koke da ‘yan uwan mamatan suka gabatarwa kwamishinan ‘yan sanda na jihar Adamawa Malam Musa Kimo dauke da hotunan matasan lokacin da suke raye a caji ofis na Kiri da kuma na gawarwakinsu da aka yiwa daurin goro kwance kan uwar madatsar ruwa na Kiri.
Mahaifan wadanda aka kashe Mal. Kunuri Hampeto da Alhaji Bakari Kem sun shaidawa majiyar mu cewa bayaga gallazawa da barazana ga rayuwarsu lokacin da suka nemi DPO ya yi masu bayanin inda ‘ya’yansu suke, ya tozartasu biyan taran kudi sama da naira dubu dari shida da kuma shanu.
Mori Ori daya daga cikin wadanda suka sallake rijiya da baya da yanzu ke zaman gudun hijira na sama da watanni shida ya yi bayanin yadda ya kubuta ‘yan sa’o’i kamin ‘yan bangan Talum da DPO ya mika a hannunsu su kashe shi.

You may also like