Ana zargin fulani da kai hari kan wata makarantar kirista a jihar Taraba


Wasu mutane da ake zargin fulani makiyaya ne sun kai hari kan wata makarantar horar da limaman cocin katolika dake Jalingo.

Evaristus Bassey,Daraktan Caritas Nigeria wata hukuma dake karkashin cicin katolika a Najeriya, ya tabbatarwa da jaridar The Cable faruwar lamarin.

An harbi wani limamin cicin aka kuma yi wasu biyu duka ya yin Kai harin.

Wadanda aka jikkata ya yin Kai harin an kai su cibiyar kula da lafiya ta tarayya dake Jalingo inda ake musu magani.

Maharan sun kuma samu nasarar lalata motoci da kuma wasu kayayyaki mallakin makarantar.

David Misal, mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar ya tabbatarwa da jaridar The Cable faruwar lamarin.

You may also like