Ana Zargin Jami’an Tsaro da Yi wa Mata ‘Yan Gudun Hijira Fyade


 

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta fitar da wani sabon rahoto inda ta zargi jami’an tsaron Nijeriya da cin zarafin matan da rikicin Boko Haram ya raba daga gidajensu.

Rahotan ya zargi Jami’an tsaro da suka hada da sojoji, ‘yan sanda, ‘yan kato da gora da kuma shugabannin da ke kula da sansanonin ‘yan gudun hijira da yi wa mata da ‘yan mata fyade.

Kungiyar ta kuma bayyanan yadda wasu daga cikin matan suka shaida mata cewa sai da aka dura masu kwayoyi kafin ayi lalata da su, yayin da wasu kuma suka ce yaudararsu aka yi da kudi da kayayyaki.

Kungiyar ta bayyanan cewa a watan Yulin bana ma sai da ta tattara bayanan mata guda 43 wadanda ke zauna a sansanin ‘yan gudun hijira a Maiduguri da jami’an tsaron suka ci zarafinsu.

A don haka ne kungiyar ta dora alhakin al’amarin akan gwamnatin Nijeriya, wacce ta zarga da kin daukan mataki game da kuma gazawa wajen baiwa matan kulawar da ta kamata.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like