Ana zargin mutane 11 yan gidan sarautar Saudiyya  da Laifin almubazzaranci da kuma aikata cin hanci da rashawa


Wani jami’in gwamnati ya ce , cin hanci, halarta kudin haram, barnatar da kudade na daga cikin zarge zargen da akewa yiwa yayan gidan sarautar Saudiyya 11 waɗanda aka kama.

Jami’in ya ce yan gidan sarautar 11 , ministoci 4 da kuma wasu tsofaffin ministoci masu yawa aka kama da yammacin ranar Asabar bayan wata doka da sarki Salman ya fitar ta kafa kwamitin yaƙi da cin hanci da rashawa wanda yarima mai jiran gado Salman Bin Muhammad zai jagoranta.

An dai bawa sabon kwamiti iko sosai da ya haɗa da binciken cin hanci da rashawa, bayar da umarnin tsare mutum, hana tafiye-tafiye, da kuma kwace kadarori.

Cikin wadanda aka tsare har da shahararren mai kudin nan dan ƙasar wato Alwaleed bin Talal wanda ake zargi da haramta kudaden haram.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like