Ana Zargin Timipre Sylva Da Amfani Da Takardun Makaranta Na Bogi
A makon jiya ne Timipre yayi murabus daga mukaminsa na minista domin yin takarar.

Ana zargin Sylva da amfani da takardun shedan karatu na bogi da kuma satar bayannan wani. Sannan, Silva ya bukaci sauya sunanshi a ranar 12 ga watan Mayun bara.

Idan ba a manta ba, Timipre Sylva ya rike mukamin gwmannan jihar Bayelsa tsawon shekaru 5 tsakanin shekarar 2007 zuwa 2012. Kafin gwamnatin Buhari ta bashi Minista a wa’adinsa na biyu, mukamin da yake rike da shi har zuwa makon da ya gabata da yayi murabus.

Tsohon sakataren labaran jam’iyyar APC Timi Frank ne ya aikewa Majalisar tarayyar Najeriyya takardar da ya bukaci Majalisar Dattijai karkashin jagorancin Ahmad Lawan ta gayyace shi domin amsa tambayoyi a game da banbance banbancen sunayen dake takardun shedar kamala karatun dan siyasar.

Takardar shedar karatun sa na sakandare na dauke da Merlin Anagha Timipre, kazalika, takardun kamala shedar karatun digirin stohon ministan na dauke da Anagha Timipre Merlin. Lamarin nan dai ya dada sanya zargi akan Silva kasancewar takardun kamala digirinsa na biyu yana dauke da wani sunan Chief Timipre Sylva

A cikin wasikar da ya aikewa Majalisar Tarayyar Najeriya, tsohon sakataren yada labaran jam’iyyar APC Timi Framk, ya kawo misalan banbance-banbancen da ke tattare da takardun shedar kammala karatun Timipre Sylva daga firamari, sakandare., digirin farko da na biyu.

Frank yayi bayani a cikin wasikar da ya aikewa majalisar tarayya cewa; abun tambaya shine me yasa sunayen da yayi amfani da su a matakan karatu daban-daban suka banbanta kuma wanene wannan chief Timipre Sylva, wanene Anagha Timipre Merlin, wanene merlin Anagha Timipre kuma wanene Anagha Timipre.

A cikin wasikar tasa, ya bukaci hukumar INEC, CCB da duk wadanda suka binciki Sylva gabanin tabbatar da shi a matsayin Minista.

Bugu da kari mai korafin, a cikin wasikar da ya aikewa Majalisar , ya bukace ta da gayyato tsohon Ministan da kuma jami’an makarantun da Sylva ya halarta domin tabbatar da sunayen da suka sanya akan takardun shedar kammala karatun da suka ba Sylva.

Makarantun sun hada da Ubis University a Switzerland, WAEC, Ajeromi Central School dake Apapa da kuma jami’ar Patakwal.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like