
Asalin hoton, AFP
Ana zargin wata mata a Enugu da ke kudu maso gabashin Najeriya da laifin kashe mai aikinta ‘yar shekara goma.
Rahotanni sun bayyana cewa matar mai suna Madam Uju ta kashe maikinta Precious Korshima tare da jefar da gawarta a wani daji.
Samun labarin mutuwar Precious ya sanya mahaifinta Jerry B Achirkpi ya shiga shafukan sada zumunta, inda yake rokon a yi mata adalci.
Mista Achirkpi ya ce Madam Uju da ya bai wa ‘yarsa domin ta yi mata aikace-aikacen gida ita ce da bakinta ta fadi ta kashe Precious tare da jefar da gawarta a daji.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Enugu Police Daniel Ndukwe, ya tabbatar wa sashen BBC Igbo faruwar lamarin, ya kuma ce suna gudanar da bincike.
Achirkpi ya ce a watan Maris din 2022 ya dauki ‘yarsa ya mikawa Madam Uju.
Ta yi masa alkawarin za ta sanya yarinyar a makarantar boko, yayin da za ta dinga taimaka mata kula da jaririn da ta haifa.
“Ƴata na hannun Madam Uju har zuwa watan Nuwambar shekarar nan da ke gab da karewa ta 2022, wani mutum ya kira ni ta layin wayar Uju, ya ce min sun sace ta hadi da ‘yata, sannan za mu biya naira miliyan 20 kudin fansa kafin su sake su,” in ji Achirkpi.
“Ranar 15 ga Nuwamba, dan uwan Uju ya kira ni ta waya tare da shaida min an sake su.
Lokacin da a kira Uju sai ta shaida min masu garkuwa da mutanen sun harbe ‘yata Precious kuma na same su a ofishin ‘yan sanda da ke New Heaven.”
Mahaifin Precious ya ci gaba da cewa, bayan kwanaki kadan, sai Uju ta sake kiransa a waya ta shaida ma sa ita ce ta kashe ‘yarsa ba tare da saninta ba.
”Da na tambaye ta ina gawar take, sai ta ce min tsoro ya sanya ta jefar da ita a dajin da ke kusa da babbar hanyar Ituku-Ozalla.”
Mista Achirkpi, ya ce ‘yan sanda sun ce lokacin da suka isa wurin da Madam Uju ta ce ta jefar da gawar Precious, ba su ga komai ba amma sun ga wani abu da ya yi kama da mutum da aka kona.
Sun ce mutanen kauyen sun ce dagacinsu ne ya ba su umarnin su kona gawar sakamakon mummunan warin da ta ke yi.
Me ‘yan sanda ke cewa?
Rundunar ‘yan sandan jihar Enugu ta bakin kakakin ta Daniel Ndukwe, ya tabbatarwa da BBC faruwar lamarin, kuma tuni suka kama wadda ake zargi da kisan Precious.
”Kawo yanzu ba san takamaimai abin da ya faru ba. Amma muna bincike, abin da sakamako ya ba mu da shi za mu yi aiki. Bai dace mu fara magana da ‘yan jarida ba tare da kammala bincike ba.”
Dokokin Najeriya kan kare hakkin yara
Najeriya na da wasu dokoki da aka gindaya domin kare hakkin yara daga cin zarafi.
Akwai dokar da kare hakkin yara ta shekarar 2003, da aka sake nazarinta a shekarar 2015.
Akwai kuma wata doka da aka fitar a shekarar 2017, karkashin Majalisar Dinkin Duniya kan cin zarafin yara da sauran cin zarafi.
Dokar ta haramta sanya yara aikin karfi, ko azabtar da su da hana su zuwa makaranta.
Dokar ta ce kowanne yaro ya na da dama da ‘yancin sanya masa suna, da ‘yancin yin wasa, da samun ingantacciyar kiwon lafiya, d sauransu.
Sai dai duk da wannan doka, a iya cewa ba bu wanda ke amfani da ita, domin yara na samun kansu cikin cin zarafi ta hanyoyi da dama a Najeriya, kuma ba a kai rahotannin hakan, idan ma an kai ba a hukunta masu aikata lafin.