
Tsantseni da gaskiya da rikon amanar ahalin gidan Shugaban Nijeriya, Muhammadu buhari ya shiga halin shakku bayyan da kungiyar nan mai fafutakar tirsasa gwamnati kan nemo da dawo da ‘yan matan Chibok wato Bring back Our Girls BBOG ta zargi daya daga cikin ‘yar Shugaba Muhammadu Buhari mai suna Hadiza Buhari-Bello da amfani da sunan kungiyar wajen tattara kudade don ‘yan matan Chibok din
Kungiyar ta BBOG ta fitar da wata sanarwa a jiya Litinin, 16 ga watan Oktoba, 2016 dauke da sa hannun jagororin kungiyar, Aisha Yesufu da Oby Ezekwesili da ke nesanta kanta daga wani taro da aka gabatar don kaddamar da asusun tallafawa ‘yan matan Chibok bisa jagorancin kungiyoyin “Peace Corps Of Nigeria” da kuma “Africa Support And Empowerment Initiative”. Kungiyoyin da ‘yar shugaba Buhari, Hadiza Buhari-Bello ke jagoranta.
BBOG ta bayyana kidimarta bisa yadda a wajen taron aka rangada tambarin kungiyar #BringBackOurGirls ba tare da sanar da su game da taro ko kuma neman izini ba.
BBOG ta bayyana cewa ba ta da hannu ko masaniya da wannan taro na kaddamar da asusun tallafi ga ‘yan matan Chibok kuma ba da amincewar kungiyar aka yi amfani da sunanta ba. A saboda haka ta ke kira ga jama’a da su ankara da wannan shiri mai cike da alamu na zargi.
“Kungiyar ta ci gaba da cewa “Bayan daukar tsawo kwanaki 902 muna fafutukar ganin an samo ‘yan matan, abin takaici ne wasu su yi amfani da wannan kokari namu wajen cimma wata manufa tasu”
“Mun samawa kanmu suna a idon duniya sakamakon aiwatar da tafiya tsakani da Allah ba tare da bin wasu don su bamu kudaden gudanar da ayyukanmu ba. Wannan shi yasa kungiyarmu ta ke kungiyar al’umma ba kungiyar wani ko wasu ba”
Mun kuma yi umarni ga lauyoyinmu, Femi Falana & Co da su dauki mataki akan wannan yunkuri da wasu ke don bata sunan kungiyarmu ta hanyar siyasantar da ita da mayar da ita hannun wasu ta yadda za a iya yin amfani da kungiyar da wata manufar ba manufar kafa ta ba.
Zuwa yanzu dai bamu da tabbacin adadin kudin da aka tara a wancan taro
cc:Alummata