Andre Gomez ya koma FC Barcelona


andre-gomes-barcelona

 

 

Dan kwallon balencia da ya kasance daya daga cikin ’yan kwallon Fotugal da suka lashe kofin Nahiyar Turai a bana Andre Gomez ya samu nasarar komawa kulob din FC Barcelona a kan Yuro miliyan 35.

Yarejejeniyar ta nuna dan kwallon mai shekara 22 ya sanya wa kulob din hannu ne a kwantaragin shekara biyar.
dan kwallon wanda yake yin kwallo a tsakiyar fili (Midfielder) ana sa ran zai haskaka a kakar wasa ta bana da za a fara a watan gobe.

You may also like