Angela Merkel ta killace kanta bayan likitanta ya kamu da Coronavirus


Shugabar kasar Jamus, Angela Merkel ta killace kanta bayan da ta yi cuɗanya da likitanta wanda aka gwada yana dauke da Coronavirus.

Steffen Seibert mai magna da yawun Merkel ya ce an sanar da shugaban kasar ta Jamus sakamakon gwajin ranar Lahadi jim kadan bayan da tayi taron manema labarai.

Seibert ya ce likitan ya yiwa shugabar kasar, allurar rigakafin cutar nimoniya ranar Juma’a.

Ya ce za a yiwa shugabar gwaje-gwaje a kwanaki masu zuwa kuma zata cigaba da gudanar da aikinta daga gida.

You may also like