Wasu mutane 2 mace da namiji a kasar China sun yi aure a kan wata igiyi da suka daura a kan gada wadda ke da nisan mita 180 daga kasa.
Ma’auratan ba su dakata da hakan ba, inda sai da suka yada hotunan yadda suka dinga lilo a jikin gadar.
Kamfanin Dillancin Labarai na China ya sanar da cewa, Ango da Amaryar sun yi auren a ranar masoya da China wato 9 ga watan Agusta a jihar Hunan da ke kasar.
Mutanen sun sa a dauki hotunansu a lokacinda suke lilo a jikin gadar.