Jam’iyyun adawa a kasar Kwango sun yi kira gamagoya bayansu da su fito domin ci gaba da fafutuka na nuna kin jinin gwamnatin shugaba Joseph Kabila.
Rahotanni daga kasar Kwango na cewar adadin wadan da suka rasa rayukansu a wata arangama tsakanin ‘yan adawa da jami’an tsaro ya haura 50, masu zanga-zanagar dai sun gudanar da gangamin ne a Kinshasha babban birnin kasar da nufin matsa wa shugaba Josesp Kabila lamba domin a bayyana jadawalin gudanar da zabubuka a kasar.
Gamaiyyar jam’iyyun adawa a kasar Kwango, sun yi magoya bayansu da su fito dan ci gaba da fafutuka na nuna kin jinin gwamnatin shugaba Joseph Kabila wanda wa’adin mulkinsa ke shirin kawo karshe. A shekara ta 2001 ne dai shugaba Joseph Kabila ya dare karagar mulkin kasar Kwango wanda yanzu ya ke nuna alamun neman wa’adi na biyu.