
Asalin hoton, Getty Images
Kociyan Tottenham, Antoni Conte ya koma kan aiki ranar Alhamis, bayan tiyata da aka yi masa.
Conte mai shekara 53, wanda likitoci suka yi masa tiyata a Italiya a makon jiya, bai ja ragamar wasan da Tottenham ta doke Manchester City 1-0 ba.
Ya koma Ingila ranar Laraba, sai dai ba a fayyace ko shi ne zai ja ragamar kungiyar ranar Asabar a wasan Premier da Leicester City ba.
A makon gobe Tottenham za ta ziyarci AC milan a wasan farko na ‘yan 16 da suka rage a Champions League.
Da yake karin bayani kan komawa kan aiki da Conte ya yi, mataimakinsa, Cristian Stellini ya tabbatar cewar dan Italiya ya kasance da su a wurin atisaye ranar Alhamis.
Stellini, bai ce komai kan tambayarsa da aka yi kan makomar Conte, wanda yarjejeniyarsa za ta kare a karshen kakar nan – koda yake Tottenham za ta iya tsawaita masa zuwa wata 12.
Conte ya koma Tottenham a 2021 bayan da kwantiraginsa ya karkare da Inter Milan.