Anyi Awon Gaba Da Shanu A Wasu Kauyukan Dake Zamfara Wasu da ake kyautata zaton barayin shanu ne sun yi awon gaba da shanu a kauyukan Ruwan Bore, Unguwar Mata da kuma Gora a jihar Zamfara.
A ranar Litinin din makon da ya gabata ne dai barayin suka dira a kauyen Ruwan Bore, inda suka yi gaba da shanu da dama. Suma jama’ar Gora kwana daya bayan an sace na Ruwan Bore hakan ta faru da su, sai kuma ranar Labarar da ta gabata an kara afka wata satar a garin Unguwar Mata duk a cikin karamar hukumar Gusau.
Da aka nemi jin ta bakin wadanda abun ya shafa sun bayyana takaici tare da shakku akan sulhun da gwamnatin Zamfara ta ce ta yi da masu aikata wannan aika-aika.
Wani da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa har yanzu tsugunne ba ta kare ba kan wannan matsala. 
A makonni biyu da suka gabata ne dai gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana kai matsaya da barayin.

You may also like