An Yi Garkuwa Da Shugaban Hukumar Zakka Da Wakafi Na Jihar Sokoto Tare Da Matarsa Da Kanwar Matarsa
A jiya ne wasu masu garkuwa da mutane suka sace Shugaban Hukumar Zakka da Wakafi na Jahar Sokoto wato Alhaji Lawal Maidoki da matarsa da kanwar matarsa a lokacin da suke hanyarsu ta dawowa daga Birnin Gwari wurin ta’aziyya.
‘Yan uwa musulmi, ku taimaki wannan bawan Allah da addu’o’inku na fatar alkairi.
Ya Allah, ka kubutar da wadannan bayi naka a cikin sauki ba tare da an illata su ba.