Anyi Kira Da Adaina Aurar Da Kananan Yara Mata A Arewacin Najeriya Wata kungiyar kare hakkin yan mata da kananan yara ta shirya bita a birnin Kano Inda tayi kira ga manayan malaman addini da sanya baki wajen hana aurar da kananan yara mata kafin su kammala karatun Boko.

Shugabar Kungiyar Malama Shafa Zangon Hausa tace so ma ace duk wata ya mace ko da baza tayi aiki ba to a barta ta kammala karatu har matsayin digiri na uku a jami’a, tace hakkan ne zai sa matan su iya baiwa yayansu tarbiyyar da ta wadata wajen ganin an shawo kan annobar shaye shaye da rashin tarbiya da girmama manya.

Ta nemi goyan bayan malaman wajen wa’azi domin hana samar yiwa yan yara mata wayo.

You may also like