Anyi Kira Ga Jami’an Tsaro Da Su Gaggauta Kama Aisha Buhari. 


Limamin Masallacin Izala na Farm Centre da ke jihar Kano Sheikh Isma’il Iliyasu Mangu, ya yi kira ga jami’an tsaro da su kama matar shugaban ƙasa Aisha Buhari. A yayin gabatar da huɗubar Juma’a Sheikh Mangu, ya bayyana cewa, “Ba muji daɗin hirar da mai ɗakin shugaban ƙasa ta yi ba, domin muna zargin abokan hamayyar siyasar Buhari ne suka haɗa kai da ita domin yaƙar gwamnati.

Babu adalci a kalamanta kuma zai iya harzuƙa sauran mata su bijirewa mazajensu. Kalamanta babbar barazana ne ga zaman lafiyar ƙasa, don haka muna kira ga jami’an tsaro da su gaggauta kama ta”.

You may also like