Wani Lauyan kare hakkin biladama, mazaunin Legas mai suna Mista Ebun-Olu Adegboruwa,yayi kira ga majalisar kasa, kan ta fara shirin tsige Shugaban kasa Muhammad Buhari, Saboda kalaman da yayi amfani dasu a wasikar da ya aikewa majalisar dattawa, kan tafiyarsa kasar Burtaniya domin a duba Lafiyarsa.
A wata sanarwa da yafitar a Legas,Mista Adegboruwa ,yace matakin da shugaban kasa ya yanke na cewa mataimakinsa yayi aiki a matsayin mai kula da tsare- tsaren gwamnati idan bayanan, a takaice yana nufin Osinbajo bashi da wani katabus kenan wajen gudanar da mulkin kasa.
“mai tsara gwamnati dai-dai yake da kowanne mutum a cikin gwamnati, hakan na nufin bazai iya nada mukami ba ko kuma ya hukunta wani minista da yayi ba dai-dai ba,”yace
Kalaman da Buhari yayi amfani dasu wajen rubuta wasikar sun jawo cece kuce a tsakanin yan Najeriya.
Buhari dai a takardar da ya aikewa majalisar dattawa, yace mataimakinsa zai cigaba da zama mai tsara harkokin gwamnati, mai makon mukaddashin Shugaban kasa K. amar yadda ya Saba bayyanawa a duk lokacin da zaiyi tafiya.