Anyi Kira Ga Musulmi Da Su Sanya Shugaba Buhari A Cikin Addu’o’in Su Na Sallolin Tahajjud A yayin da wannan dare mai albarka (Lailatu kadari) ke tunkaro mu, ina tunatar da ku cewa mu sanya shugaba Buhari cikin addu’o’inmu.

“Ya Allah, Mahaliccin dukkan halittu, makagin duniya, mai hukunci a ranar hisabi, Sarkin sarakuna, mahaliccin Annabi Muhammadu (S.A.W) ka dubi shugaba Muhammadu Buhari, shugabanmu, Uban kasa, ka ba shi kariya, ka ba shi ingantacciyar lafiya da karin hikima ka kuma kare shi daga sharrin masharranta.

Allah ya mun yi tawassuli da Annabi Muhammad (S.A.W) da Al Kur’ani, ya Allah Ka karawa Shugaba Muhammadu Buhari lafiya da nisan kwana. Allah ka kare shi daga dukkan sharri.

Allah Ya biya mana bukatun mu, Ya amsa ibadun mu baki daya.
Bashir Ahmad, shine mai baiwa shugaba Buhari shawara kan harkokin kafafun yada labarai

You may also like