Anyi Kuskure Wajen Bawa Kamaru Yankin Tsuburin Bakassi – Osinbajo 


Mukaddashin shugaban kasa Yemi Osinbajo yace bawa kasar Kamaru yankin Bakassi bayan hukuncin da kotun duniya ta yanke, babban rashi ne ga Najeriya.

Da yake magana a wurin taron ganawa da Jama’a a birnin Kalaba a jiya Alhamis, Osinbajo yace gwamnatin tarayya zata taimakawa mutanen Bakassi da hukuncin ya rabasu da mutsugunansu.

Ya kuma ce gwamnati zata binciki abin da yake faruwa tsakanin mutanen Bakassi, Sojoji da kuma masu tada kayar baya a yankin. 

 ” Damkawa Kamaru yankin Bakassi da Kotun sasanta rikici ta duniya tayi wani abin cigaba ne da dukkan mu mukayi amanna cewa babban rashine,”mukaddashin shugaban kasar yace. 

” Amma shugaban kasa Muhammad Buhari ya yarda cewa yayin da muke cigaba da tattauna batun shari’ar,baza mu  taba barin yan Najeriya da suke zaune a Ikang da sauran wurare su cigaba da shan wahala.

 “Gwamnatin tarayya tabbas zata yi wani abu akai tare da ganawa da mutanen Bakassi. Wannan shine aikin mu kuma shine abinda muka kudiri yi. ”

Yace gwamnatin tarayya tana da son jihar ta Kuros Riba wannan yana daga cikin hangen nesan shugaba Buhari wajen hada kai da jihar domin samar da damarmaki ga mutanen jihar. 

Mataimakin Shugaban kasar ya samu rakiyar ministan man fetur, Ibe Kachiku,Pastor Usani Ughuru ministan yankin Neja Dalta, da kuma shugabar ma’aikata ta tarayya Winfred Oyo-Ita.

You may also like