Anyi wa Yahoo kutsen imel milliyan 500


Masu satar bayanai ta Internet sun kutsa cikin sakonnin email na masu amfani da dandalin Yahoo, inda suka saci bayanai daga email din mutane miliyan 500.
Wannan dai ba shi ne karon farko da irin hakan ya taba faruwa ba domin ko a 2014 hakan ya faru.

Kutsen dai ya hada da satar bayanan da suka jibanci sunaye da imail-imail da kuma tambayoyi da amsoshin sirri.

Sai dai kuma kamfanin ya ce kutsen bai shafi bayanan sirri na katin cire kudi.

Kamfanin ya kara da cewa kutsen ba zai rasa nasaba da irin hannun da wasu kasashe ke da shi ba a lamarin.

A watan Yuli ne dai kamfanin Verizon ya sayi Yahoo a kan kudi $4.8bn.

Hukumar Binciken cikin gida ta Amurka wato FBI ta ce tana binciken badakalar.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like