Anyiwa Wasu Mafarauta 18 Kisan Gilla A Jihar Zamfara


Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta tabbatar da cewa kimanin mutane 18 suka rasa rayukansu a kauyen Birane da ke karamar hukumar Zurmi bayan arangamar tsakanin mafarauta da ‘yan Fashi.

Kakakin Rundunar, Muhammad Shehu ya ce, al’amarin ya auku ne a lokacin da mafarautar suka cafke wani makiyayi wanda suke zargin ya sato Shanu amma kuma ya samu ya arce inda ya je ya gayyato ‘yan uwansa daga karamar hukumar Isa da ke cikin jihar Sokoto wadanda suka yiwa mafarautar kwantar bauna tare da kona gawarwakinsu bayan da suka hallaka su. Ya ce, rundunar na ci gaba da bincike kan lamarin.

You may also like