APC bata yi adalci ba wajen kafa kwamitin sake duba fasalin Kasa


Kungiyar Musulmai kare hakkin Musulmai ‘MURIC’ ta kalubalanci jam’iyyar APC kan yadda ta kafa kwamitin da zai sake duba yadda za a sake lalo shirin gudanar da mulkin da rabon arzikin Kasa.

Kungiyar wanda Ishaq Akintola ke shugabanta ta ce duk da cewa jihohin yan kabilar Igbo duk jam’iyyar PDP ce ke mulki ya kamata ace an saka koda shugabanni jam’iyyar ne na jihohin a cikin kwamitin ba a yi watsi da su ba.

Ishaq ya ce idan ba a manta ba su yan kabilar Igbo din ne suka fara maganar hakan kuma har yanzu sune suke korafi akan yadda fasalin kasa yake da neman abasu kasarsu.

“ Saboda haka ya dace ace akwai wani nasu a cikin kwamitin.” Inji Ishaq

“Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai ne zai jagoranci kwamitin inda gwamnonin Osun, Rauf Aregbesola, Kano, Abdullahi Ganduje, Filato, Simon Lalong, Ogun , Ibikunle Amosun, tsohon gwamnan jihar Edo, Oserheimen Osunbor, sakataren jam’iyya , Osita Izunaso, Bolaji Abdullahi da Olubunmi Adetunmbi.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like