
Asalin hoton, Getty Images
Atiku Abubakar (na biyu daga dama) ne ya yi wa PDP takarar shugaban ƙasa a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, wanda kotu ta bai wa Bola Tinubu na APC nasara
Babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya, ta bayyana hukunce-hukuncen da kotunan ɗaukaka ƙara suka yi, inda suka ƙwace nasarar wasu gwamnoni a matsayin “karan-tsaye” ga dimokraɗiyya.
Jam’iyyar adawar na zargin APC mai mulkin Najeriya ne da “amfani da ƙarfin iko” wajen tanƙwara hukuncin kotunan, zargin da APC ta musanta.
“Shari’ar Najeriya ta zama kamar rawar ‘yan mata yanzu; idan an yi gaba, sai a koma baya,” in ji Mataimakin Sakataren PDP na Ƙasa, Ibrahim Abdullahi.
A makon jiya ne, kotunan ɗaukaka ƙara suka yanke hukuncin soke nasarar gwamnoni uku na jihohin Filato, da Zamfara, da Kano – dukkansu a arewacin ƙasar. PDP ce ke mulki a jihohin Zamfara da Filato, yayin da NNPP ke mulkin Kano.
Hukuncin kotunan ya bai wa hukumar zaɓe ta Inec umarnin ƙwace shaidar cin zaɓe daga hannun Gwamnan Filato Caleb Mufwang, kuma ta bai wa Nentawe Goshwe na APC.
A Zamfara kuma, kotun ta ɗaukaka ƙara ta soke halascin zaɓen Gwamna Dauda Lawal Dare na PDP tare da bayar da umarnin a sake zaɓe a wasu ƙananan hukumomi na Maradun da Birnin-Magaji da kuma Bukkuyum.
PDP ta ce akwai wasu hujjojin da ba su kai waɗanda ta gabatar ƙwari ba a baya, amma kuma yanzu aka yi watsi da su a shari’o’in da ta kai.
“A gwamnatinmu ta PDP [a baya] an sauke wasu gwamnoni bisa hujjojin da ba su ma kai waɗanda muka gabatar muni ba [a yanzu], amma kuma aka yi watsi da su,” kamar yadda Ibrahim Abdullahi ya bayyana.
Sai dai jam’iyyar APC mai mulki ta musanta zargin, tana mai cewa “shure-shure ne da ba shi hana mutuwa”.
“Shari’ar nan ba a ɗaki aka kulle aka yanke hukunci ba, alƙalai ne suka yi aiki da hankali da kuma abin da shari’a ta ce,” a cewar kakakin APC na ƙasa Bala Ibrahim.
Cecekucen na zuwa ne yayin da magoya bayan gwamnan Filato suka hau tituna don gudanar da zanga-zangar nuna ƙin amincewa da hukuncin kotun a birnin Jos ranar Lahadi.
Wasu masana shari’a a Najeriya sun soki shari’o’in na Kano, Zamfara, da Filato. Daga cikinsu akwai ƙwararren lauya Femi Falana, wanda ya nemi a sake duba hukuncin.
Kazalika, rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta yi gargaɗin hukunta “masu shirin shirya zanga-zanga bayan samun wasu bayanai da ke nuna cewa wasu ƙungiyoyin magoya bayan jam’iyyu na yunƙurin shiryawa domin nuna ɓacin rai kan hukuncin kotun”.
Hukuncin kotun ya ce Abba bai cancanci zama ɗan takarar gwamna ba, saboda shi ba dan jam’iyya ba ne.