APC na Daf dayin Nasara a zaben Jihar Edo


Yanzu Haka APC Ta Baiwa PDP Ratan Kuri’u Dubu 5,616
Hukumar zabe ta bayyana sakamakon zaben kananan hukumomi 9 cikin 18 a zaben gwamnan jihar Edo.
Sakamakon ya nuna cewa jam’iyya mai mulki, APC ta yi nasara a kananan hukumomi biyar yayin da PDP ta yi nasara a kananan hukumomi hudu.
Kawo yanzu dai APC na da adadin kuri’u dubu 142,424 yayin da PDP take da kuri’u dubu 136,808.
Hakan ya nuna cewa dan takarar APC Godwin Obaseki, ya baiwa babban abokin karawarsa na PDP, Osagie Ize-Iyamu ratar kuri’u dubu 5,616.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like