APC Reshen Legas Ta Yi Fatali Da Matakin Tsawaita Wa’adin Shugabannin Jam’iyyar


Jam’iyyar APC reshen jihar Legas ta yi fatali da matakin da kwamitin zartaswar jam’iyyar na kasa ya dauka na tsawaita wa’adin shugabannin APC tun daga matakin tarayya zuwa na jihohi inda ta nuna cewa hakan ya saba tsarin mulkin Nijeriya.

Shugaban Jam’iyyar APC na Legas, Tajudeen Olusi ya ce sashe na 223 na kundin tsarin mulkin Nijeriya ya tanadi gudanar da zabuka na maye gurbin shugabannin jam’iyyar da wa’adinsu ya cika inda ya ce, za su mika korafinsu ga Shugaban kasa. A makon da ya gabata ne dai kwamitin zartaswar APC ya karawa shugabannin jam’iyyar wa’adin shekara guda.

You may also like