APC ta nada El-Rufai shugaban kwamitin duba batun sake fasalin Najeriya


Jam’iyyar APC ta nada kwamitin mutane tara a karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, domin su duba batun sake fasalin Najeriya.

A cikin wani jawabi a rubuce da kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi ya sa wa hannu, ya ce jam’iyyar ta kafa kwamitin ne a yayin taron hukumar gudanarwar ta na biyar da kuma taro da gwamnonin jam’iiyyar.

Sauran mambobin kwamitin sun hada da gwamnan Edot Oserheimen Osunbor, Bolaji Abdullahi, Osita Izunaso da kuma wani sanata da zai zama sakataren kwamitin.

Sanarwar ta ce ‘Jam’iyyar APC ta lura da cewa tada kurar da ake yi domin a kawo sauti ya fara daukar salon a fara karkar kasa.

“Dangane da haka ne a yayin taron da shugabannin gudanarwar APC su ka yi da gwamnoni, aka yanke cewa a kafa kwamiti domin a ya yi duba kan lamarin.

Shi kuma shugaban jam’iyyar APC, John Odigie-Oyegun, ya bayayyana cewa idan ana so a san matsayin jam’iyyar a kan batun sake fasalin kasar nan, to a sake karanta kundin manofofin jam’iyyar a natse.

Dangane da wannan batu, Mukaddashin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin su wadda ke karkashin tutiyar jam’iyyar APC, saisaita al’amarin.

You may also like