Rahotanni daga jihar Ekiti sun tabbatar da cewa Ministan Sinadari, Kayode Fayemi ne ya lashe zaben fidda- da- gwani na ‘yan takarar kujerar Gwamnan jihar Ekiti na karkashin tutar jam’iyyar APC.
Ministan dai ya samu kuri’u 941, sai kuma tsohon Gwamnan jihar, Segun Oni wanda ya samu kuri’u 481. ‘Yan takara 33 ne dai suka fafata a zaben fidda gwani don neman a tsayar da su takarar kujerar Gwamnan jihar Ekiti wanda za a gudanar a ranar 14 ga watan Yuli.
Tun da farko dai, an soke zaben fidda gwani bayan wata hatsaniya da aka yi na rashin jituwa tsakanin ‘yan takarar kafin daga baya shugabannin jam’iyyar su sulhunta al’amarin. Ministan dai ya taba zama Gwamnan jihar kafin Gwamnan na yanzu, Fayose ya kwace kujerar daga hannunsa.