APC Ta Tsayar Da Tambuwal A Matsayin Dan Takarar Gwamnan Sokoto


Jam’iyyar APC reshen jihar Sokoto ta tsayar da Gwamnan jihar, Aminu Waziri Tambuwal a matsayin dan takararta a zaben 2019.

Shugaban APC na jihar, Alhaji Usman Suleman ya ce sun yanke shawarar tsayar da Tambuwal ne bayan sun gamsu bisa ayyukan ci gaban kasa da ya aiwatar a jihar don haka suke son ci gaba da ba shi goyon baya saboda dorewar wadannan ayyukan.

You may also like