APC Ta Yi Raddi Ga Ministar MataSabanin ikirarin da Ministar Mata, Aisha Alhassan ta yi kan cewa Shugaba Buhari ya yi alkawarin yin wa’adin mulki guda ne, Shugaban jam’iyyar APC na Kasa, Cif John Odigie-Oyegun ya ce Shugaba Buhari ne kadai zai yanke hukunci Akan ko zai yi tazarce ko kuma Wa’adi guda zai yi kan karagar mulki.

Ya ce, a halin yanzu Buhari na da muhimman batutuwa a gabansa na ganin tattalin arzikin kasar nan ya bunkasa ta yadda Talaka zai samun saukin rayuwa inda ya nuna cewa idan lokaci ya yi Shugaba Buhari zai bayyana wa al’ummar Nijeriya shawarar da ya yanke game da makomar siyasar sa.

You may also like