Jam’iyyar APC ta tsara kashe Naira Bilyan 14.82 a kasafin kudinta na wannan shekarar inda ta tsara samun wadannan kudade ta hanyar sanya haraji ga ‘ya’yan jam’iyyar da ke rike da mukamai da kuma gudanar da gidauniyoyi sannan da kudin sayar da katin zama dan jam’iyya.
A bisa tanadin kasafin kudin, jam’iyyar ta tsara kashe Naira Bilyan 1.96 wajen mallakar ofishinta na kasa, sai Naira Bilyan 1.3 wanda za ta kashe wajen gudanar da Babban taronta na kasa. Haka ma, ta ware milyan 400 don harkokin zabe da kuma Naira Bilyan 500 wanda za ta sayo Motoci da su.