A madadin daukacin shugabannin hukumar gudanarwar Arewa24news tare da sauran wakilai da masu ba da gudunmawa wajen tafiyar da wannan kamfani, muna bayyana farin cikin mu da zagayowar ranar haihuwar shugaban kasa kuma babban kwamandan askarawan Nijeriya, Muhammadu Buhari.
Muna addu’ar Allah Ubangiji Ya kara masa lafiya da tsawon kwana. Kuma da karin hikima da kwarin gwiwar cigaba da tafiyar da harkokin mulki da sha’anin rayuwar ‘yan Nijeriya.