Arsenal da Chelsea na zawarcin Williams, Mourinho na son koma wa Bayern MunichJose Mourinho

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jose Mourinho

Arsenal da Chelsea na cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan gefen Athletic Bilbao Nico Williams a lokuta da dama, inda ake ganin dan wasan dan shekara 21 a matsayin wanda ya dace da gasar Firimiya. (Fabrizio Romano, via CaughtOffside)

Kawo yanzu dan wasan gaban Paris St-Germain Kylian Mbappe mai shekara 25, bai amince da sharuddan komawa Real Madrid ba idan kwantiraginsa ya kare yayin da kulob din na La Liga ke kokarin cimma matsaya da mahaifiyar dan wasan Faransa kuma wakiliyarsa, Fayza Lamari. (Marca)

Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya nuna alamun kungiyarsa ba ta bukatar Mbappe saboda tuni ta samu ‘zakakuran ‘yan wasa 6 a duniya’ (Goal)

Dan wasan AC Milan Francesco Camarda zai rattaba hannu kan kwantiraginsa na farko na kwararru da kungiyar Rossoneri a lokacin da matashin dan kasar Italiya ya cika shekara 16 a watan gobe duk da cewa Manchester City da Borussia Dortmund na sha’awarsa (Calciomercato, via Football Italia)Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like