Arsenal na tangal-tangal a kokarin lashe PremierArsenal ta tashi 2-2 a gidan West Ham United a wasan mako na 31 a gasar Premier League ranar Lahadi.

Hakan ya sa Arsenal wadda ke jan ragamar teburin Premier na sassarfa a shirin da take na lashe Premier a karon farko bayan 2003/04.

Gunners ce ta fara cin kwallo biyu, kan hutu West Ham ta zare daya, sannan ta farke na biyu a wasan na hamayya na kungiyoyin birnin Landan.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like