
Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta mika goron zawarcin dan wasan tsakiya na Ecuadur Moises Caicedo kan fam miliyan 70, amma Brighton na son saida dan wasan mai shekara 21 kan fam miliyan 80. (Mail on Sunday)
Arsenal din dai za ta yi kokarin sayo dan wasan tsakiya na Ingila da West Ham Declan Rice, mai shekara 24, a kakar wasa ko da sun yi nasarar soyo Caicedo. (Telegraph – subscription required)
Newcastle da Tottenham ka iya sayan mai kai hari na Belgium Romelu Lukaku, mai shekara 24, wanda a yanzu haka ya ke buga wasa a Inter Milan a matsayin aro daga Chelsea. (Calciomercato – in Italian)
Tottenham na bibiyar dan wasan Everton kuma mai tsaron ragar Ingila, Jordan Pickford, mai shekara 28, gabannin musayar ‘yan wasa a kaka mai zuwa. (Football Insider)
Nottingham Forest na duba yiwuwar dauko dan wasan tsakiya na Amirka da Juventus Weston McKennie, duk da ta bayyana karara Leeds United na zawarcinsa. (Athletic – subscription required)
West Ham ta bi takwararta Aston Villa a kokarin dauko dan wasan Marseille kuma na tsakiyar Faransa Matteo Guendouzi, mai shekara 23. (Metro)
Fulham ta mika sabuwar bukatar dauko dan wasan tsakiya na Brazil, mai taka leda a Fluminense Andre, mai shekara 21, a matsayin bashi. (Fabrizio Romano)
Bournemouth na shirin taya sayan dan wasan Fenerbahce da Najeriya, Bright Osayi-Samuel, mai shekara 25, kan farashin fam miliyan. (Sun on Sunday)
Everton ta nuna sha’awar sayan dan wasan Southampton, mai kai harin Scotland Che Adams, mai shekara 26. (Football Insider)
Aston Villa da Crystal Palace za su biya fam miliyan 25, idan har su na son dauko dan wasan Watford na tsakiyar Senegal Ismaila Sarr, mai shekara 24. (Sun on Sunday)