Arsenal ta barar da damar cin Liverpool a Anfiel a karon farkoPremier League

Asalin hoton, Getty Images

Liverpool da Arsenal sun tashi 2-2 a wasan mako na 30 a gasar Premier League da suka buga ranar Lahadi a Anfield.

Minti takwas da fara wasa Arsenal ta ci kwallo ta hannun Gabriel Martinelli, minti 20 tsakani Gabriel Jesus ya kara na biyu.

Kwallon da Martinelli ya ci na 25 a Premier League kenan, ya zama na biyu daga Kudancin Amurka, bayan Gabriel Jesus da ya yi wannan bajinta masu shekara 21 da haihuwa.

Karon farko da Arsenal ta ci Liverpool kwallo biyu a Anfield a Premier League tun Satumbar 2012 a karawar da Gunners ta yi nasara da ci 2-0.Source link


Like it? Share with your friends!

2

You may also like