
Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta dauki dan kwallon tawagar Poland, Jakub Kiwior daga Spezia mai buga Serie A kan yarjejeniya mai tsawo.
Mai shekara 22 zai bayar da gudunmuwar da Mikel Arteta ke bukara, wajen lashe Premier League da fuskantar kalubalen kakar nan.
Dan wasan Brazil, Gabriel ya yiwa Gunners dukkan karawar Premier League kawo yanzu, kenan Kiwior yana da kwarewar da zai iya buga gurbin idan an samu matsala.
Kiwior ya buga wa Poland karawa tara har da wasa hudu a gasar cin kofin duniya da aka yi a Qatar a 2022.
An nuna hotonsa a Emirates tare da Edu daraktan wasannin Arsenal a lokacin da Gunners ta ci Manchester United 3-2 a gasar Premier League ranar Lahadi.
Kiwior shi ne na biyu da Arsenal ta dauka a watan Janairun nan, bayan Leandro Trosssard daga Brighton kan fam miliyan 21.
Kiwior ya fara taka leda a matakin kwararren dan wasa a Zeleziarne ta Slovakia a 2019 daga nan ya koma MSK Zilina kaka daya tsakani.
A cikin watan Agustan 2021 ya koma Spezia kan yarjejeniyar kaka hudu da rabi.